News
An bude dagar Neja ta biyu domin saukaka tafiye-tafiye a lokutan bukukuwan sabuwar shekara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamatin tarayya ta bayar da umarnin bude gadar Neja ta biyu domin matafiya da ababan hawa su yi amfani da ita, domin saukaka zirga-zirga a yankin kudu maso gabas a lokutan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar Shekara.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta gina gadar bayan shafe gomman shekaru tana cikin yanayi na lalacewa da kuma Ababan hawa kan kwashe tsawon kwananki cunkushe saboda rashin kyawunta.
Babbar gadar dai ta kasance wacce take hada kudu maso gabashin kasar da sauran jihohi dake makwabtaka.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, wanda ya ba da wannan umarni a ranar Laraba a wajen kaddamar da gadar, ya ce za a bude gadar domin amfani da ita na tsawon wata daya a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara mai kamawa.
Minista Fashola ya ce manufar Shugaba Muhammadu Buhari na kammala gadar ita ce ceton rayuka da kuma rage radadin talauci da lokaci mai tsawo da ake bata-wa kan tsohuwar gadar Neja ta farko.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da cewa tunda an gama gadar ya kamata a samar da hanyar shiga ta yadda a lokacin hutu zasu ci gajiyar wannan muhinmin gyara da aka yi kan gadar.
Hukumomin sufuri a kasar sun kayyade gudun kan hanyoyin Najeriya shine kilomita 100 a cikin sa’a guda.
Saboda haka gwamnati za ta ji dadi idan masu amfani hanyoyi na tuka motocinsu cikin natsuwa da kiyayewa a lokacin amfani da wannan hanya musamman a lokutan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Gwamnatin kasar ta bayar da tsawon kwanaki talatin ana cin gajiyar ko yiwa mutane alakoro kafin a sake rufe babbar gadar a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2023, domin ci gaba da aiwatar ayyukanta da suka dan rage.
