Connect with us

Labarai

Rasha ta yi wa Ukraine luguden hare-hare

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

 

Ukraine ta ce tara daga cikin cibiyoyin samar da wutar lantarkin ta sun lalace a wasu manyan sabbin hare-haren makamai masu linzami na Rasha, kuma yawan makamashin da ake amfani da shi a kasar ya ragu da fiye da rabi.

Advertisement

Akwai wuce gona da iri kan batun ‘yan ci rani a Qatar

An bayar da rahoton cewa, hare-haren da aka ce sun kai akalla sittin, sun kashe akalla fararen hula uku a tsakiya da kuma kudancin Ukraine. A birni na biyu mafi girma a kasar wato Kharkiv, babu wutar lantarki.

 

BBC ta rawaito cewa  yanayi ne mai wahala ake ciki a Kyiv, ana ta kankara, mutane a nan da sauran garuruwa na cikin mawuyacin hali.

 

Ana fargabar baraguzai sun danne wasu, yayin da wani makami mai linzami ya dira a wata majalaisa da mutane ke hutawa a birnin Kryvyi Rih da ke tsakiyar kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending