Connect with us

News

Dattawa Sun Kashe Matashi Domin Tsafi A Zariya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Dubun wasu tsofaffi hudu ta cika kan zargin su da yi wa wani matashi kisan gilla da yukurin cire sassan jikinsa domin tsafi a Zariya dake Jihar Kaduna.

 

Advertisement

Aminiya ta gano cewa matashin mai suna Emmanuel Pius mai shekara 29, daga garin Warri na Jihar Delta, ya gamu da ajalinsa ne bayan ya ziyarci mahaifiyarsa a Zariya.

 

Advertisement

Yadda Tankar Mai Ta Yi Bindiga Ta Kone Shaguna Da Gidaje

Mahaifiyarsa, Sarah Pius, ta shaida wa Aminiya cewa bayan isowarsa da kwana biyu ne ya fita da niyyar zuwa banki ciro kudi, daga nan ba a kara jin duriyarsa ba.

 

Advertisement

Ta ce an yi ta kokarin kiran shi ta waya amma ba a samun shi, har rubutaccen sako an tura amma haka ba ta  cim-ma ruwa ba.

 

Advertisement

 

“Daga nan ne na tafi wurin ’yan sanda don kai rahoto a babban ofishinsu da ke PZ, Sabon Gari, Zariya.

Advertisement

 

“Ina wurin ne sai na sami waya daga Ofishin ’Yan sanda na Samaru inda suka bukaci in je wurinsu.

Advertisement

 

“Bayan na je sun sa na koma na zo da dan uwan mahaifin yaron, inda suka sanar da shi cewa wasu dattawa gudu hudu ake zargi da kashe Emmanuel.

Advertisement

 

“Sun sanar da shi cewa wadanda ake zargin suna hannunsu…har sun nuna mini su kuma dukkansu dattawa ne wadanda sun yi jika da yaron,” in ji ta.

Advertisement

 

 

Advertisement

Sarah Pius ta shaida wa wakilinmu cewa wadanda ake zargin sun yi yunkurin yanke wasu sassan jikin dan nata, amma Allah Bai ba su sa’a ba.

 

Advertisement

Sai dai duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin ’yan sanda game da lamarin bai yi nasara ba.

 

Advertisement

Ya kira Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ta waya, amma ya ce masa yana halarar wani taro, zai kira daga baya.

 

Advertisement

Sai dai har ya zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton babu wani karin bayani, duk da cewa har sake tuna  mishi aka yi, amma shiru.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending