Connect with us

News

Gwamnati ta amince PDP ta gudanar da taro a babban filin wasa na Katsina

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

Gwamnatin jihar Katsina ta sahalewa jam’iyyar adawa ta PDP gudanar da babban taronta domin yakin neman zaɓen dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar a babban filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina.

Advertisement

 

 

Advertisement

A cikin wata takarda daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar mai dauke da sa hannun Sulaiman Kankia, babban Sakatare a ofishin mai kula da harkokin siyasa, gwamnatin ta ce bayan kammala ‘yan gyare-gyaren da aka yi wa filin wasan, yanzu an sahale wa jam’iyyar PDP din ta gudanar da wannan taro.

Yan Tuwita sun bukaci Elon Musk ya sauka daga shugabancin kamfanin

Tun da farko jam’iyyar PDP a jihar Katsina ta koka bisa abin da ta kira rashin adalci na hana ta yin taro a babban filin wasa na Katsina.

Advertisement

 

 

Advertisement

Jam’iyyar dai ta nemi gwamnatin jihar da ta ba ta aron filin wasa na Muhammad Dikko domin gudanar da gangamin yakin neman zaɓen dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar.

 

Advertisement

Jam’iyyar ta hannun Daraktan Janar na yakin neman zaɓen Atiku Abubakar a jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa ta ce ta rubuta a hukukance tana son a ba ta aron wannan filin wasa domin gudanar da wannan taro amma aka hana ta.

 

Advertisement

 

Mustapha Inuwa ya ce sun yi la’akari da aikin gadoji da ake yi cikin gari da yadda taron zai kasance idan aka kai shi kusa da manyan asibitocin Katsina amma duk da hakan gwamnati ta yi mursisi ta hana su.

Advertisement

 

Da farko dai, sai da gwamnatin ta fitar da wata takarda daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar, ta ba da dalilanta na hana PDP taro a wannan filin wasa, da ta ce ana wasu ‘yan gyare-gyare ne shi ya sa ba a samu damar ba jam’iyyar filin ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

Idan za a tuna dai, a zamanin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Shema a jam’iyyar PDP ne aka kammala ginin filin wasan bayan da marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya fara dora gina ta lokacin yana Gwamnan jihar. Sai dai yanzu gwamnatin APC ke mulki a jihar ta Katsina.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending