News
Kotu ta yanke wa Doyin Okupe shekaru 2 a gidan yari
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
A yau Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Doyin Okupe, tsohon babban mataimaki na musamman, SSA kan harkokin yaɗa labarai ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Doyin Okupe, daurin shekaru biyu a gidan yari.
Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, a hukuncin da ta yanke, ta samu Okupe da laifuka 26 daga cikin 59 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta shigar a kansa kan laifin satar kudi.
Gwamnati ta amince PDP ta gudanar da taro a babban filin wasa na Katsina
Mai shari’a Ojukwu ya bayar da umarnin cewa tuhume-tuhume 26, wadanda suka janyo wa Okupe zaman gidan yari na shekara biyu kowanne, za su gudana a lokaci guda.
Alkalin kotun, ya bayar da zabin Naira 500,000 a kowanne daga cikin tuhume-tuhumen, wanda adadinsu ya kai Naira miliyan 13, wanda dole ne a biya kafin karfe 4:30 na yamma a yau.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, mata da ƴaƴan Okupe sun nemi a yi masa sassauci bayan an yanke masa hukuncin.
-
Uncategorized7 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News2 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
