News
Boxing Day: Yadda aka samo sunan ranar washe garin Kirsimeti da asalinta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
“Boxing Day” – rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti – ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekarun 1800.
Ranar ba ta da wata alaƙa da wasan damben boxing da ake gudanarwa a faɗin duniya.
BBC ta rawaito cewa Sunan ya samo asali ne sakamakon ƙunshe kyauta da masu arziki ke yi a cikin akwati kafin su bai wa mabuƙata – ‘box’ na nufin akwati a harshen Hausa.
Boxing Day a al’adance, ita ce ranar da bayi kan yi hutun aiki sannan su karɓi kyautuka na musamman daga iyayen gidansu.
Haka nan, a ranar ce su ma suke zuwa gida domin bai wa iyalansu akwatunan kyautar.
Advertisements
