News
Rwanda ta ce jiragen yaƙin DR Kongo sun rasa sararin samaniyarta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Rwanda ta ce jiragen yaƙin DR Kongo sun ratsa sararin samaniyarta yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar tashin hankali tsakanin maƙwabtan ƙasashen biyu kan ayyukan ‘yan tayar da ƙayar baya a gabashin DR Kongo.
A wata sanarwa da gwamnatin Rwanda ta fitar ta ce ”jirgin yaƙin DR Kongo ya saɓa wa sararin samaniyar ƙasarmu inda ya yi shawagi ta ɓangaren tafkin lardin Kivu da ke yammacin ƙasarmu”.
To sai dai daga bi-sani jirgin ya koma DR Kongo kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ko a watan da ya gabata ma dai wani jirgin yakin DR Kongo marar ɗauke da makamai ya sauka a filin jirgin Rwanda a kusa da kan iyakar ƙasar, a wani abu da DR Kongo ta bayyana da cewa hatsari ne.
Rwanda dai ta ce wannan saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ƙulla a ƙasashen Angola da Kenya.
DR Kongo dai na ci gaba da zargin Rwanda da taimaka wa ‘yan tawayen M23, zargin da Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka da Fransa da Belgium ke goyon baya.
Zargin da ita kuma Rwandan ta sha musantawa a lokuta da dama.
