Politics
Taron Kano Ya Tabbatar Da Cewa Tinubu Ba Shi Da Wani Abin Da Zai Tsinanawa Yan Najeriya – Atiku
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce ganin yadda Tinubu ya gaza yin wata magana mai daukar hankali gaban jama’a a jihar Kano, ya nuna ba zai yi wa ‘yan Nijeriya abin kirki idan ya gaji shugaba Buhari ba.
A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Phrank Shaibu ya fitar, Atiku Abubakar ya bayyana haka ne bayan Tinubu ya tara jama’a a Kano yayin gangamin yakin neman zaben sa.
Rahotanni sun ce, bayan an kashe makudan kudade wajen shirya taron gangamin a Kano, Tinubu ya kasa fadin wata magana mai ma’ana a wajen taron.
Sanarwar ta cigaba da cewa, maimakon Tinubu ya yi magana mai ma’ana, sai ya rika tikar rawa a bainar nasi wanda hakan ya tabbatar babu abinda zai iya tsinanawa yan Najeriya a cewar sanarwar.
