Connect with us

News

Tsohon mijin Funke Akindele ya Musulunta

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Tsohon mijin Funke Akindele ya dawo Musulunci, inda ya ce ‘na ɓata amma na dawo kan turba’

 

Advertisement

AbdulRasheed Bello, wanda aka fi sani da JJC Skillz, ya bayyana cewa ya dawo Muslunci, addininsa na asali da ya bari.

KANO:Kotu ta bada umarnin a kamo dan mai unguwa bisa zargin fasa idon wata amarya

Marubucin waƙa kuma mai shirya fina-finai, wanda ya lashe lambobin yabo da dama, ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na Instagram, @JJCSkillz.

Advertisement

 

Bello, wanda tsohon mijin jarumar fim ne, Funke Akindele, ya ce an haife shi a cikin Musulmi amma bai taɓa aikata addinin ba sabo da ya na bin addinin mahaifiyarsa.

Advertisement

 

“Na ɓata, amma yanzu na dawo hanya madaidaiciya, Ya Allah, ina neman gafararKa a duniya da lahira. Ya Allah ina rokonka lafiya a cikin lamurana na addini da na duniya, da iyalaina da dukiyata.

Advertisement

 

“Ya Allah ka lullube ni da raunina, kuma ka saukaka mini bacin rai, kuma ka kiyaye ni daga gaba na da baya da damana da haguna da sama, kuma ina neman tsarinka don kada kasa ta hadiye ni.

Advertisement

 

Mawakin a wata hira da wata kafar yada labaran addinin musulunci ta yanar gizo, Muslim News, ya ce Allah ne Ya sa a karshe ya musulunta, yana mai cewa addinin ya sa shi a hanya madaidaiciya da kuma mai da hankali.

Advertisement

 

“An haife ni Musulmi ne—AbdurRasheed. Babana Bello Musulmi ne, amma mahaifiya ta Kirista ce. A lokacin ina zuwa islamiyya, amma ina tuna cewa ana zane ni idan na je. Sun kasance suna tsoratar da mu da wutar jahannama, don haka ban taba aikata bauta ta Addinin Musulunci ba.

Advertisement

 

Allah ne Ya ƙaddara zan dawo addinin Musulunci.” Na gode wa Allah da Ya tseratar da raina,” inji shi.

Advertisement

 

“Na yi farin ciki da na sake samun Musulunci saboda ya ba ni kwanciyar hankali. Ya ba ni jagora da mai da hankali. Na ɓata, amma yanzu na dawo,” ya kara da cewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending