Labarai
Kasar Italiya ta haramta amfani da manhajar GPT

An haramta amfani da ƙirƙirarriyar basira da ke kwaikwayon halayyar ɗan adam ta ChatGPT.
Hukumar da ke lura da lamuran bayanai na intanet ta ce manhajar na da barazana.
Masu ƙirƙira na Amurka ne suka samar da ita a matsayin mafari kuma tuni Microsoft suka zuba hannun jari ciki.
Hukumomin sun ce sun dakatar da amfani da manhajar ne ba tare da bata wani lokaci ba, kuma za ta yi bincike a kai cikin gaggawa.
Manahajar tana amsa tambayoyin da ɗan adam ke da su a ransa, kuma tana kwaikwayon yadda mutum yake rubutu da wasu abubuwan na daban.
Microsof an kashe bilioyin dala kan wannan manhaja da ake bincike kanta inda fara aiki da ita a watan jiya.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
