News
Ƙungiyar gwamnonin ta yi Allah wadai da masu shirin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya
Ƙungiyar gwamnoni ta yi Allah wadai da kakkausar murya ga masu yunƙurin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, a maimakon rantsar da shugabannin da aka zaɓa a ƙasar.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ƙungiyar ta ce za ta yi duk mai yiyuwa domin kare martabar dimokraɗiyyar ƙasar.
Kungiyar TUC ta gargaɗi gwamnatin Najeriya kan cire tallafin man fetur
Haka kuma ƙungiyar ta ce ba za ta goyi bayan duk wani abu da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar ba.
Gwamnonin sun ce fitar da sanarwar cewa akwai masu yunƙurin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ba tare da kama masu shirin ba, ka iya haifar da ruɗani da firgice a ƙasar.
Inda suka yi kira ga hukumar tsaron farin kaya a ƙasar ta DSS da ta gaggauta kama tare da gurfanar da waɗanda ke da hannun a yunkurin kafa gwamnatin riƙon ƙwaryar.
