News
Gwamnatin jahar borno Ya Tsawaita Lokacin Ritaya Ga Malaman Makaranta
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya tsawaita waadin kammala aiki ga malaman makarantu a jihar da shekaru biyar.
Hakan na kunshe ne a wata takardar da ta fito daga hukumar kula da koyarwa ta jihar Borno mai dauke da sa hannun babban sakataren hukumar Malam Yusuf Garga. Kamar yanda jaridar Punch ta rawaito.
Wata Tirela Maƙare Da Kaya Ta Ƙwace Ta Afka Masallaci A Suleja
“Gwamna Babagana Zulum ya amince da tsawaita wa’adin aiki ga daukacin malaman jihar Borno daga shekaru 35 zuwa 40 sannan daga shekara 60 zuwa 65, wanda kuma wannan sauyin zai fara ne nan take.”
“Dukkan malaman da ke da sha’awar jin daɗin wannan abu ana sa ran su rubuta wa hukumar ta hannun shugabanninsu na nuna sha’awarsu tare da haɗa takardar shaidar lafiyar jiki daga kowane asibitin gwamnati,” in ji sanarwar.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
