Politics
APC ta kori sanata Danjuma Goje bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa
Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta kori sanata Muhammad Danjume Goje bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa.
A watan da ya gabata ne jam’iyyar APC a matakin mazaɓa ta kafa wani kwamiti domin binciken zarge-zargen yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa da ake yi wa sanatan a zaɓukan 2023.
Yayin da yake yi wa manema labarai a Kashere, shugaban mazaɓa na jam’iyyar Tanimu Abdullahi, ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin korar sanatan ne bayan da kwamitinj binciken ya same shi da laifin da ake zarginsa da shi.
Ya ce “Daga cikin laifukan zagon-ƙasan da ya yi wa jam’iyyar har da rashin halartar tarukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar,”.
”Da kuma rashin halartar babban taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyar na ƙasa Abdullahi Adamu suka jagoranta”, in ji shi
