News
SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO ZAIYI NADIN SARAUTAR CIGARI A RANAR JUMA’A
DAGA KASSIM TIJJANI TURAKI.
A karon farko Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero zai nada kaninsa kuma jikan Sarkin Musulmi Abubakar na lll Dan saudatu jikar Amirul Muminina yar sarkin Musulmi Muhammadu Ballo Dan Shehu Usuman DanFodio sarauta CIGARI ranar juma’a nan mai zuwa 28 ga watan Aprilu,2023 da karfe 9 na safe a kofar kudu In Allah ya kai mu.
Sarautar Cigari ta samo asali ne tun daga Sarkin Kano Ibrahim Dabo shine sarki na farko da ake wa laqabi da Dabo cigari wanda ta hakane kanon ma itama ta samo sunanta daga lakabin sa wato KANO TA DABO CIGARI badan komi ba sai dan jarumtarsa ta yaki ance a zamaninsa ne yaci duk garurukan da suke kewayen Kano ya sa ake ce masa cigari.
Kamar yadda masana tarihi da bincike suke fada rabon da tarihi irin haka ya maimaita kansa tun zamanin Sarkin Kano Alu mai sango wanda shima jikane ga Amirul Muminina Sarkin Musulmi Alu Babba wanda shine yaci sunansa kamar yadda shima Ado Ado yaci sunan mahaifinsa Marigayi mai martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero( BABBAN DODO ) dan audu ka iya sarki Allah ya jaddada rahama gareshi shima kuma Allah yasa sunan ya bishi ya kuma rika masa sarautar.
Allah yasa ayi taro lafia!
