Connect with us

News

Ɗalibai 60,000 ne suka fuskanci matsaloli wajen rubuta jarrabawar JAMB

Published

on

 

 

Advertisement

Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun jami’o’i a kasa (JAMB) ta ce masu rubuta jarrabawar kimanin 60,000 ne suka gamu da matsaloli a cikin kwana biyun da suka wuce.

 

Advertisement

Adadin wani kaso ne a cikin mutum 947,000 da suka rubuta jarrabawar JAMB a wannan lokaci.

SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO ZAIYI NADIN SARAUTAR CIGARI A RANAR JUMA’A

Shugaba sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana haka bayan rangadin wuraren da ake rubuta jarrabawar tare da Babban Magatakardan hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede da sauran jami’ai ranar Alhamis a Abuja.

Advertisement

 

Ya ce an sake sanya ɗaliban lokacin da su je su rubuta jarrabawar tasu.

Advertisement

 

Ya ba da tabbacin cewa za a bai wa duk wanda ya yi rijista don rubuta jarrabawar JAMB dama yin hakan, yana cewa hukumar ta shawo kan matsalolin na’urorin da aka fuskanta a ranar farko ta rubuta jarrabawar a wasu cibiyoyi da ke faɗin ƙasar.

Advertisement

 

Dr Fabian Benjamin ya ce wannan ce jarrabawa mafi inganci da suka taɓa yi a tsawon shekaru, ko da yake ya san wasu za su yi jayayya da abin da ya faɗa saboda matsalolin da aka samu ranar Talata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending