News
Shugaban kasar Tinusia, Kais Saied ya kori Firai Ministar ƙasar Najla Bouden.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shugaban kasar Tinusia, Kais Saied ya kori Firai Ministar ƙasar Najla Bouden.
Ms Bouden ta kasance mace ta farko da ta fara rike mukamin, kuma daman Mr Kais ne ya zaɓe ta ba tare da bata lokaci ba lokacin da ya kori wanda ta gada shekaru biyu da suka gabata.
Shekaru biyu kenan da shugaban mai salon mulkin danniya ko mulaka’u, ke ɗaukar matakin korar manyan jami’an gwamnatinsa.
An sake dakatar da wani likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Bbc ta rawaito cewa Tuni shugaba Kais ya maye gurbinta da wani dan siyasa Ahmed Hachani, wanda ya rike babban mukami a babban bankin Tinusia.
Wannan matakin na zuwa ne daidai lokacin da ƙasar ta faɗa rikita-rikitar siyasa da durƙushewar tattalin arziki, da tsadar rayuwa, da garƙame duk mai adawa da gwamnati.
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
