Connect with us

News

An sake dakatar da wani likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Published

on

asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Shugaban hukumar kula da asibitoci a jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya sake dakatar da wani likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Ana zargin likitan ya bar aikin sa ne tsawon dare daya a ranar Litinin.

Advertisement

Gwamnatin Jihar Kano Na Shirin Fara Sayarwa Al’ummarta Kayan Abinci A Farashi Mai Rahusa

Dr Nagoda wanda ya kai ziyarar bazata da karfe 12 na dare kuma ya tafi da karfe 5 na Asuba, ya tarar da rashin likita a bakin aiki kuma bai iya samunsa ko a waya ba.

Shugaban kula da asibitocin ya koka da cewa bayan dakatarwar da aka yi wa wasu likitoci a ranar Litinin, yanasa ran cewa duk sauran likitoci da ma’aikatan jinya da ke wasu cibiyoyin lafiya zasu dauki ayyukansu da muhimmanci.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa a baya hukumar ta sauke shugabannin wasu asibitoci uku a jihar Kano inda ma’aikatan lafiya suka kauracewa ayyukansu a daren ranar 30 ga watan Yuli da ya gabata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending