Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano Na Shirin Fara Sayarwa Al’ummarta Kayan Abinci A Farashi Mai Rahusa

Published

on

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Idan kana cikin masu jiran tallafin gwamnatin jihar Kano bayan cire tallafin man fetur, to a iya cewa jira ya kare yayin da gwamnatin ta fitar da tsare-tsaren agajin rage radadi.

Sai dai ga dukkan alamu tallafin yazo cikin sabon yanayi domin gwamnatin jihar na shirin siyan hatsi daga gwamnatin tarayya da kuma sayarwa a farashi mai rahusa ga mazauna jihar ta Kano.

Advertisement

Tallafin Mai: DSS Da Yan Sanda Ne Suka Janyo Hauhawar Farashin Man Fetur -Shugaban IPMAN

Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a lokacin wani taron tattaunawa na farko da mambobin kwamitin kyautata ‘Da’a a cikin al’umma CRC daga kananan hukumomi 44 a jiya.
A bangaren sufuri kuwa, Gwamnan ya ce ana shirin farfado da motocin Kanawa domin taimakawa dalibai da mata da sauran nau’o’in mabukata kyauta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending