News
Hukumar NSCDC ta kama mutane 46 gidajen rawa a Gombe

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar tsaron farin kaya ta kasa , NSCDC, reshen jihar Gombe, a ranar Talata, ta kama wasu mutane 46 da aka kama a gidajen rawan dare, da aka fi sani da Gidan Gala,Wadanda ake zargin dai sun hada da mata 32 da maza 14.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar NSCDC, Mu’azu Sa’ad, ne yabaiya na hakan yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin, ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne bisa kin bin umarnin Gwamna Muhammadu Yahaya na cewa a rufe dukkan gidajen rawa.
Kotu Ta Hana Hukumomin EFCC, CCB Da ICPC Binke Akan Muhyi Magaji Da Hukumarsa
Ya ci gaba da bayyana cewa, “An samu wadanda ake zargin suna son aikata lalata da aikata laifuka a wadannan Gidan Gala.”
Ya ce rundunar ta samu damar tuntubar wasu iyayen wadanda ake zargin, inda ya ce za su gurfanar da su a gaban kotu.
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 9 na dare bayan umarnin da aka bayar da misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin.
An kama wadanda ake zargin a Sabon Gida BCGA, Gadan Gala dake New Mile 6, yayin da wasu kuma aka kama su a Gidan Wasa/Gidan Drama, New Mile 3, da Liji, dake kan titin Kalshingi.