News
Hukuncin Kotun Koli: Najeriya ta lalace – Atiku Abubakar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da ya gabata, Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa babu wani fata a Najeriya.
Atiku ya bayyana haka ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin wani taron manema labarai na kasa da kasa a Abuja yayin da yake mayar da martani kan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Ahamad Tinubu.
Ana zargin wani matashi da kisan karamin yaro tare ƙwaƙwule masa Idanu a Kano
Daily Post ta rawaito cewa Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce daga baya tarihi zai tabbatar da yunkurinsa na dakile nasarar Tinubu.
“Idan har kotun koli, wacce ita ce kotun koli a Najeriya, za ta yi watsi da kukan ‘yan Najeriya duk da hujjoji, to Nijeriya ta yi hasarar ta, kuma kasar ta lalace.
“Na tabbata cewa tarihi zai tabbatar da hakan. Babban asara ba nawa ba ne, ‘yan Najeriya ne,” inji shi.
A wani labarin kuma Ana zargin wani matashi da kisan karamin yaro tare ƙwaƙwule masa Idanu a Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
