Connect with us

News

Yunƙurin juyin mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Rahotanni daga ƙasar Guinea na nuni da cewa, ana zargin yunƙurin juyin mulki a ƙasar bayan da aka jiyo ƙazamar musayar wuta a Conakry, babban birnin ƙasar, a ranar Asabar.

Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jami’an tsaro sun yi wa yankin ƙawanya, ba shiga ba fita.

Gwamanatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 15 Domin Gyaran Gadar Jahar Legas

Wata majiya da aka sakaya sunanta ta ce, “Ana musayar wuta daga tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tare da harba makaman yaƙi a Kaloum.”

“Tun da asuba aka kulle garin, ba shiga, ba fita,” in ji wani ɗan kasuwa a yankin.

Advertisement

Guinea na ɗaya daga jerin ƙasashen da suka fuskanci juyin mulki tun 2020. Sauran ƙasashen sun haɗa da Mali, Burkina Faso, Nijar da kuma Gabon.

Shugaban sojojin juyin mulki a Guinea, Kanal Mamady Doumbouya, ya karɓe ragamar shugabancin ƙasar ne a ranar 11 ga Satumban 2021 bayan da ƙasar ta shafe shekara 11 kan turbar mulkin farar hula.

A wani labarin Gwamanatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 15 Domin Gyaran Gadar Jahar Legas

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending