Connect with us

News

Ku Guji Manyan Otal A Najeriya, Amurka Ta Gargadi ‘Yan Kasarta

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Amurka ta fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan kasarta da ke Najeriya da su guji manyan otal-otal a kasar, saboda wata barazanar tsaro da ake zargin kai wa wadannan otal-otal a manyan biranen kasar.

Amurka ta ba da wannan gargadin a cikin wani sako na hukuma ga ‘yan Amurkan mai kwanan wata 3 ga watan Nuwamba.

Gwamanatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 15 Domin Gyaran Gadar Jahar Legas

Ya ce ‘yan kasar Amurka su rika sanya ido a manyan otal-otal, su rika lura da abubuwan da suke kewaye da su, su rika hulda da su, sannan su yi bitar shawarwarin tafiye-tafiye ga Najeriya kafin su shiga otal.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Amurka tana sane da sahihan bayanai da ke nuna cewa akwai babbar barazana ga manyan otal-otal a manyan biranen Najeriya. Jami’an tsaron Najeriya na aiki tukuru domin dakile wannan barazana.”

Advertisement

Sanarwar ta kuma bayar da adireshi da lambobin wayar ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da ofishin jakadancin da ke Legas idan duk wani dan Amurka yana bukatar taimako.

A halin da ake ciki kuma, shugaban kungiyar masu gudanar da yawon bude ido ta Najeriya, Ime Udo, a ranar Asabar ya tabbatar wa ‘yan kasashen waje cewa Nijeriya ta kasance cikin zaman lafiya don ziyartar yawon bude ido da kasuwanci.

Udo na maida martani ne kan gargadin da Amurka ta yi wa ‘yan kasarta a Najeriya da su guji manyan otal-otal a kasar saboda barazanar rashin tsaro.

Da yake magana a wata hira da ya yi da jaridar PUNCH a ranar Asabar, Udo ta bayyana cewa kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta bai isa ya hana bakin kasashen waje ziyara ba.

Ta kara da cewa, “Babu wata kasa da ba ta da kalubale na musamman. Amurka na daya daga cikin kasashen da a kodayaushe suke son kare al’ummarta komai kankantarta ko babba, amma ba za ku iya amfani da hakan a matsayin ma’auni cewa Najeriya ba ta da aminci ga baki ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending