News
Ba Zamu Maimata Kuskuren Biyan Jami’nmu Ba A Wannan Karon-INEC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara biyan karin alawus-alawus na kashi 40 cikin 100 da gwamnatin tarayya ta amince.
Mista Yakubu ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan hukumar a Yenagoa a ziyarar da suka kai domin tantance shirye-shiryen zabe a jihar.
Kamfanin Dangote ya zargi BUA da daukar nauyin yada labaran karya akansa
A watan Afrilu ne gwamnatin tarayya ta sanar da karin kashi 40 cikin 100 na alawus alawus da ake biyan ma’aikatan gwamnati.
Na san da yawa daga cikinku ba su ji dadi ba saboda ba ku sami alert na kudi kashi 40 na tallafin da ake baiwa dukkan ma’aikatan gwamnati ba domin rage wahalhalun da tattalin arzikin da ke fama da shi na cire tallafin man fetur inji Yakubu.
Ya bayyana cewa ma’aikatan za su samu alawus-alawus kafin zaben ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo.
PREMIUM TIMES ta rahoto cewa Mista Yakubu a ranar Laraba ya kare Naira biliyan 18 da aka ware wa INEC a cikin karin kasafin kudin bana.
A wani labarin kuma Kamfanin Dangote ya zargi BUA da daukar nauyin yada labaran karya akansa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
