News
EFCC Ta Gabatar Da Tsohon Gwamnan CBN A Gaban Kotu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A ranar Litinin 6 ga Nuwamba, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar ta gabatar da tsohon gwamnan ko doka ta yi aiki a kanta.
Ana zargin Emefiele da badakalar kuɗi da wasu ƙumbiya-ƙumbiya da suka shafi sake fasalin Naira da wasu ayyuka da aka gudanar na bunƙasa tattalin arziki a ƙarƙarshinsa.
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
