Connect with us

News

Yakin Israila Da Hamas Na Barazanar Haifar Da Yakin Duniya Na 3 -Kawu Sumaaila

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Majalisar dattawa ta bukataci gwamnatin taraya ta hada hannu da sauran kasashen duniya domin kiran a tsagaita wuta a rikicin Israila da kuma Hamas.

Sunce rikicin yana tunawa da yakin basasan da akayi a Najeriya da kuma irin tashin hankalin da yan Najeriya suka fuskanta sakamakon yakin, inda majalisar ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta sake yin duba akan tsarin samar da kasa biyu a yankin domin magance matsalar rikicin Israila da Palastinu.

Kashe Rayuka Da Karya Dokokin Yaƙi A Gaza, Dole Mu Yi Magana Majalisar Dattawan Nigeria

A wani kudiri da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaaila daga Kano ya tsara, aka kuma gabatar da shi jiya Talata a gaban majalisar bayan zazzafar muhawara, yanzu dai baki ya haɗu wajen neman Najeriya ta bayyana matsayarta a rikicin na Gaza.

 

Advertisement

Majalisar Dattawar ta bayyana mace-mace da kuma adadin waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Isra’ila da Hamas a matsayin abin tsoro.

A tattaunawarsa da BBC Sanata Kawu Sumaila ya ce sun yi la’akari da abubuwan da suke faruwa sun kai maƙura da ya kamata Najeriya ta bayyana matsayarta kan wannan rikici.

‘Yan majalisar sun jadada bukatar samar da zaman lafiya a yankin tare da gujewa fadawa yakin duniya na uku.

Kudurin dai ya samu goyon bayan ‘yan majalisa kusan 45, waɗanda suka sama hannu gabainin a gabatar da shi gaban Majalisa.

A wani labarin kuma Kashe Rayuka Da Karya Dokokin Yaƙi A Gaza, Dole Mu Yi Magana Majalisar Dattawan Nigeria

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending