Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Jarabawar Makarantu Saboda Yajin Aiki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta dakatar da jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire a jihar sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka yi.

Jaridar Inda Ranka  ta ruwaito cewa NLC da TUC sun fara yajin aikin a ranar Talata da tsakar dare a fadin kasar nan.

Za a janye ƴan sandan da ke bai wa manyan jami’an gwamnati tsaro a Najeriya

A ranar Talata 14 ga watan Nuwamba, 2023 ne aka shirya gudanar da jarabawar, amma yanzu an dage jarabawar har abada.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ma’aikatar Ilimi ta Jiha, ta dakatar da Jarrabawar cancantar Sakandire ta 2023 (SSCE) da aka shirya gudanarwa a yau, Talata, 14 ga Nuwamba, 2023, har sai an samu sanarwa.”

Sanarwar mai dauke da sa hannun Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar, Balarabe Abdullahi Kiru, ta yi kira ga dalibai da iyaye/masu kulawa da su jure duk wata matsala da dakatarwar ta haifar.

Advertisement

Hakazalika, bankuna, asibitoci, da sauran wuraren taruwar jama’a a jiha

A wani labarin kuma Za a janye ƴan sandan da ke bai wa manyan jami’an gwamnati tsaro a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending