News
Zaben Gwamnan Jihar Kano : ‘Yan sanda Sun Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Yunkurin Tayar Da Hargitsi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dangane da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano za ta yanke, kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Muhammad Usaini Gumel, FIPMA, tare da sauran shugabannin hukumomin tsaro da ke aiki a jihar, sun tura isassun jami’ai da kayan aiki don jan kunne ga ‘yan siyasa masu yunkurin tayar da hargitsi.
An tura jami’an ne a wurare masu mahimmanci a cikin jihar don tabbatar da tsaro na rayuka da dukiyoyi da kuma dakile duk wani yunkuri na haifar da hargitsi ko rashin bin doka da oda.
Yajin Aiki: TCN ta Musanta Rahoton Datse Wutar Lantarki A Fadin Nijeriya
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da jami’in hulda Jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, 2023.
CP Gumel ya kara nanata cewa, rundunar ‘yansanda tare da sauran jami’an tsaro a jihar ba za su daga kafa ba ga duk wani da ke kokarin kawo cikas ga tsarin tsaro ba, don haka ake kira ga mazauna jihar, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.
A wani labarin kuma Yajin Aiki: TCN ta Musanta Rahoton Datse Wutar Lantarki A Fadin Nijeriya
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
