News
Kotun daukaka kara ta karɓe nasarar gwamnan jihar Plateau, Caleb Muftwang, Caleb Mutfwang.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotun daukaka kara da ke zamanta a babban Birnin tarayya Abuja ta karɓe nasarar gwamnan jihar Plateau, Caleb Muftwang na jam’iyyar PDP..
Wani kwamiti mai mutane 3, a wani hukunci na bai-daya a yau Lahadi, ya ce Muftwang bai bi ka’ida ba wajen tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP kamar yadda sashe na 285(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Mayakan Houthi sun sha alwashin kai hari kan duk wani jirgin ruwa na Isra’ila
Kwamitin ya kara da cewa karar da Nentawe Goshwe na jam’iyyar APC ya kawo ya samu nasara saboda batun cancantar zabe ne na gaba da bayan zabe, a karkashin sashe na 177(c) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da sashe na 80 da 82 na Dokar Zabe, 2022..
Kotun ta umarci INEC da ta karɓe satifiket din zabe daga hannun Muftwang ta kuma baiwa Goshwe sabo.
