Connect with us

News

Sauke Abba Kabir daga mulki barazace ga rayuka da dukiyoyin Yarabawa mazauna Kano -Ƙungiyar Yarabawa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Ƙungiyar Yarabawa mazauna jihar Kano sun baiyana fargabar cewar idan har Kotun Koli ta kori Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf to fa za a iya kai musu hari.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Sakataren Ƙungiyar Yarabawa mazauna jihar Kano Taofeek Olalekan Olaosebikon ne ya baiyana hakan a taron manema labarai a jiya Alhamis a Kano.

Advertisement

Kotun Daukaka Kara ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi, ta Bada Umarnin Sake Sabon Zabe

Ya kara da cewa muna kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kada ya yi katsalandan a kan batun shari’ar zaɓen gwamnan jihar Kano.

A cewar Olaosebikon, an fara raɗe-raɗin cewa da hannun Shugaban kasa a kokarin da ake na kwace kujerar Gwamnan jihar kano, inda ya ce hakan ka iya zama barazana ga rayuka da dukiyoyin Yarabawa mazauna Kano.

Advertisement

Ya yi kira ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da sauran sarakunan Yarabawa a fadin ƙasar nan da su tsawatar wa Tinubu kan yunƙurin tumbuke gwamnatin jihar.

 

Advertisement

“Kowa ya ga cewa Abba ne ya ci zaɓe. To duk wani yunkuri na yin muna-muna ba zai haifar da ɗa mai ido ba kuma mu Yarabawa abin zai shafa tunda shugaban kasar namu ne beyerabe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending