Connect with us

News

An Kone Sama Da Tan 15 Na Miyagun Kwayoyi A Jihar Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, data magance matsalolin cikin gida take kawo mata tarnaki wajen yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Advertisement

Gwamnan ya yi wannan roko ne ta bakin shugaban Ma’aikatansa, Shehu Sagagi a yayin kona Tan 15 da digo 7 na miyagun kwayoyi da hukumar ta NDLEA ta yi.

Akalla jarirai 10 suka mutu dalilin fama da tsananin yunwa a sansanin ‘yan gudun hijira dake Abuja – Kungiya

Ya ce samun wasu mutane a cikin hukumar da ke yiwa hukumar zagon kasa ta hanyar hada baki da masu dillancin miyagun kwayoyi, na komar da kokarin gwamnati baya na yaki da matsalar.

Advertisement

Haka zalika gwamnan ya jaddada kudirin jihar nan na yaki da matsalar shaye-shaye ta hanyar samar da cibiyoyin koyar da sana’oi domin sauya matasa daga kan wannan halaiyya.

A wani labarin kuma Akalla jarirai 10 suka mutu dalilin fama da tsananin yunwa a sansanin ‘yan gudun hijira dake Abuja – Kungiya

Advertisement

An shiga rana ta biyar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, bayan Qatar da ke shiga tsakani ta sanar da tsawaita wa’adin da sa’o’i 48, domin samun damar musayar ƙarin fursunoni tsakanin bangarorin biyu.

Ofishin Firaiministan Isra’ila ya ce an ba su sunayen Isra’ilawa 10 da Hamas za ta saka a yau Talata, wanda ta yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.

Advertisement

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya yi maraba da wannan labari inda ya ce yana fatan wannan tsagaita wuta zai sanya mutane su koma cikin hankalinsu, da fahimtar tashin hankali da amfani da karfin soji ba za su magance matsalar ba.

Ita ma Isra’ila ta bada sunayaen Falasdinawa mata 50 da ka iya samun ‘yanci kafin karewar wa’adin a ranar Alhamis.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending