News
Rundunar ’yan sandan ta cafke wata mata bisa zargin sheka wa mijinta ruwan zafi saboda bai je biki da ita ba a Legas
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta cafke wata mata mai bisa zargin sheka wa mijinta ruwan zafi saboda bai je biki da ita ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Litinin.
Jamhuriyar Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa
Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Disamba, inda aka kama wadda ake zargin bayan da rundunar ta samu labarin faruwar lamarin.
Ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma mijin matar na kwance a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Tun da farko wata majiya ta shaida wa NAN cewa matar ta fusata da mijin, wanda ya halarci daurin auren abokinsa amma ya ki tafiya da ita.
NAN ta ruwaito cewa rikici ya barke a tsakanin ma’auratan, lamarin da ya kai ga matar debo tafasasshen ruwan zafi ta kwara wa mijin nata.
Tun da fari ma’auratan sun shirya zuwa wurin bikin tare, amma daga baya mijin ya sauya shawarar tafiya shi kadai kamar yanda Aminiya ta ruwaito
A wani labarin kuma Jamhuriyar Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
