Connect with us

News

Kungiyar SERAP Ta Maka Kamfanin Man Fetur Na Kasa NNPCL A Kotu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Kungiyar SERAP mai fafutukar Kare Hakkokin Tattalin Arziki da tabbatar da demokradiyya ta maka kamfanin man fetur na kasa NNPCL a gaban sharia, kan rashin bayyana cikakkun alkaluman yadda ake hako mai da safarar sa a kullum da kuma yawan kudaden shiga da ake samu daga man fetur tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun shakerar nan.

A kwanakin baya ne dai tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Sunusi Lamido Sanusi ya yi zargin cewa kamfanin na NNPCL ya gaza samar da isassun kudaden kasar waje a cikin baitul malin kasarnan duk da cire tallafin man fetur.

Advertisement

Rundunar ’yan sandan ta cafke wata mata  bisa zargin sheka wa mijinta ruwan zafi saboda bai je biki da ita ba a Legas

Kungiyar ta SERAP dai na neman kotu ta ba da umarni tare da tilastawa kamfanin na NNPCL da ya bayyana cikakkun bayanai kan gangunan man da Najeriya ke hakowa da kuma wadanda take fitar da su a kullum da kuma yawan kudaden shigar da ake samu tun bayan cire tallafin man fetur.

SERAP tana kuma neman kotu ta tilastawa kamfanin na NNPCL ya bayyana cikakkun bayanai na biyan Naira Tiriliyan 11 da aka biya a matsayin tallafi man fetur daga 1999 zuwa Mayu 2023, gami dayin cikakken bayanin yadda aka salwantar da kudaden. Sai dai kawo yanzu ba a kayyade ranar da za a saurari karar ba.

Advertisement

A wani labarin kuma Rundunar ’yan sandan ta cafke wata mata  bisa zargin sheka wa mijinta ruwan zafi saboda bai je biki da ita ba a Legas

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending