News
Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Karbi Mutane 66 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Sokoto ta karbi mutane 66 da dakarun rundunar Operation Hadarin Daji suka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar.
Sawaba radio ta bayar da labarin yadda hadakar dakarun rundunar suka yi nasarar kubutar da mutane 52 da aka yi garkuwa dasu a karamar hakumar Isa dake jihar Sokoto.
Zaben Cike Gurbi: APC Za Ta Sayar Da Takardar Tsayawa Takarar Sanata Naira Miliyan 20
Da yake jawabi yayin mika wadanda lamarin ya shafa kwamadan runduna ta 8 na sojin Najeriya, birgediya janar Alex Tawasimi, yace dakarun sun gudanar da wani samame ta kasa wanda ya kai ga ceto mutanen aka kai Dajin Gundami, bayan watanni 3 da sace su.
Gwamnan jihar ya tabbatar da yunkurin gwamnatinsa na tallafawa jami’an tsaro domin aikin dawo da zaman lafiya da kwaciyar hankali a jihar. Haka kuma gwamnan tare da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sun bayar da Naira miliyan 16.6 ga mutane 66 da sojoji suka kubutar daga hannun masu garkuwa a tsakanin ranar alhamis zuwa asabat.
