Connect with us

News

An rantsar da Aiyedatiwa gwamnan Ondo, hadiman marigayi Akeredolu uku sun yi murabus

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Babban alkalin jihar Ondo Olusegun Odunsola ya rantsar da mataimakin gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa sabon gwamnan Ondo.

A jawabinsa na farko, gwamna Aiyedatiwa ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku, sannan za a sauko da tutoci a faɗin jihar.

Shehu Sani ga gwamnoni: Ku dena ɗiban kuɗin talakawa ku na kai wa Tinubu gaisuwa a jiragen haya  

Akeredolu ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba bayan fama da ya yi da rashin lafiya na ɗan tsawon lokaci.

Gwamnan ya ce zai ci gaba da yi wa al’umman jihar Ondo aiki kamar yadda marigayi tsohon gwamna Akeredolu ya ya lokacin yana raye.

Premium Times ta ruwaito cewa Rasuwar Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, SAN, CON

Advertisement

hakika babban rashi ne a gare ni a matsayina na amininsa na kud da kud kamar yadda dangantakarmu ta samo asali tun shekaru da dama da suka gabata, kasancewar mun yi aiki tare da shi lokacin da ya fara neman zama gwamna a shekarar 2012.

A Wani labarin kuma Shehu Sani ga gwamnoni: Ku dena ɗiban kuɗin talakawa ku na kai wa Tinubu gaisuwa a jiragen haya  

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending