Connect with us

News

Ƴan ta’adda sun dasa bam a maƙabarta, sun halaka masu zaman makoki 103, sun jikkata wasu 141

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRAD’YAN

 

Ƴan ta’adda sun dasa bam a maƙabarta, sun halaka masu zaman makoki 103, sun jikkata wasu 141

Mahukuntan ƙasar Iran sun bada sanarwar cewa wani harin bam da aka kai kan masu zaman makokin jimamin tuna shekaru takwas da kisan Babban Kwamandan Dakarun Juyin Juya Hali, Janar Qassem Soleimani, ya hallaka mutum 103, tare da jikkata wasu mutum 141.

Kudin Kananan Hukumomi: Kotu Ta Bai Wa Gwamnatin Kano Wa’adin Kwana 7

An kai harin a wata maƙabarta, a Iran a ranar Laraba, inda dandazon masu jimami suka taru domin addu’o’i da jimamin kisan da Amirka ta yi wa Soleimani shekaru huɗu da suka gabatar.

Premium Times ta ruwaito cewa Mahukuntan ƙasar dai sun ce ‘yan ta’adda ne suka ɗana bam ɗin. Haka dai jami’ai a Kerman suka tabbatar.

Advertisement

Sanarwar ta ce tattakewar da aka yi wa mutane a wurin rincimin gudu ne ya haifar da yawan waɗanda suka jikkata a harin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Tasmin ya ruwaito cewa bam biyu aka tasa, kuma a cikin jakar matafiya aka isa da bam a maƙabartar.

Mahukuntan ƙasar sun ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar jimami, tare da jaddada cewa za a kamo waɗanda suka aikata wannan ta’addanci a hukunta su.

A wani labarin kuma Kudin Kananan Hukumomi: Kotu Ta Bai Wa Gwamnatin Kano Wa’adin Kwana 7

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending