Connect with us

News

Dattijuwar Kaza mafi tsufa a duniya ta mutu tana da shekara 21

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

 

Dattijuwar Kazar nan da tafi kowacce Kaza tsufa a duniya mai suna “Peanut” ta mutu tana da shekaru 21 a duniya.

Peanut dai ita ce Kazar da ta ke rike da kambun duniya (Guinness World Record), wajen yawan shekaru a cikin jinsinta na Kaji a duniya.

Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Waɗanda Ake Zargi Da Satar Shanu A Kaduna

Rahotanni sun ce Peanut ta mutu ne a ranar 25 ga watan jiya na Disamba wato a ranar Kirsimeti, a wani gidan gona da ke Michigan a kasar Amurka tana da shekara 21 da kwanaki 238.

Advertisement

Mista Marsi Darwin wanda shine mutumin da ya mallaki Kazar Peanut, ya fitar da sanarwa cikin alhini na mutuwar Peanut, inda ya bayyana ta a matsayin wani bangare na rayuwarsa.

A wani labarin kuma Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Waɗanda Ake Zargi Da Satar Shanu A Kaduna

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending