Business
Manyan Dalilai Da Suka Sa Johan Rupert Wawurewa Ɗangote Kambun Wanda Yafi Kowa Kuɗi A Nahiyar Afirka -Masana

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI
In ba a Manta ba a ƴan kwanakin da suka shuɗe ne jaridar fobres ta fitar da gwarzon nahiyar Afirka wanda dama wannan abu ne da aka saba yi duk shekara,Sai dai wani abin mamaki da ya yi matakur bawa mutane alhini shine rikitowar shahararren mai kuɗin nan na Najeriya wato Alhaji Aliko Ɗangote . Ɗangote dai fiye da shekaru goma kenan yana rike da wannan kambu na wanda ya fi kowa kuɗi a Nahiyar Afirka,Amma kash a shekarar nan ne aka sami wani mashahuran attajiri ɗan ƙasar Afirka ta kudu Johan Rupert inda ya doke Ɗangote ya wawure wanna kambu .
A wani binckike da TRT Afrika Hausa tayi ta yi dubi ga wasu dalilai da ake ganin su ne suka zamo chikas wa Ɗangote.
Abu na farko akwai Mummunar faɗuwar darajar Naira,kowa dai yasan yadda Naira tayi faduwar baƙar tasa,Naira ta yi faɗuwar da ba taɓa gani ba.
Masana tattalin arziki sun ce karyewar darajar Naira na ɗaya daga cikin abubuwan da suka yi tasiri sosai wajen raguwar kuɗin Dangote.
Dakta Isa Abdullahi na tsangayar Tsimi da Tanadi na Jami’ar Kashere a jihar Gombe a wani zantawa da TRT Afrika ta Yi da shi ya shaida cewar bayan karyewar Naira,Lalacewar hannun jari a Najeriya suma sun taka babbar rawar gani;Dakta Isa ya cigaba da cewa ana auna yawan kuɗin attajiri ne musamman irin su Dangote bisa darajar zunzurutun kuɗi, hannayen jari da kuma kamfanoni da suka mallaka.
A wani labarin kuma Yan Ta’adda Sun Yi Wa Matar Aure Yankan Rago A Jihar Yobe
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu