Connect with us

News

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Fatattaki  Shugabannin FCCPC, BPE

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaba kasa  Bola Ahmad Tinubu ya kori manyan jami’an hukumar kula da gasa ta tarayya (FCCPC), Mista Babatunde Irukera da Darakta-Janar  da Ofishin Kamfanonin Gwamnati (BPE), Mista Alexander Ayoola Okoh.

Advertisement

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai  Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an umurci shugabannin da aka kora da su mika ragamar yakin su ga  manyan jami’ai a hukumominsu, har sai an nada sabbin shugabannin zartarwa.

Kisan Nafi’u: Kotu Ta Dage Shari’ar Hafsat Chuchu

Fadar shugaban kasar ta ce bisa wannan umarnin na shugaban kasa, tsige su daga mukamansu ya fara aiki nan take.

Advertisement

A wani labarin kuma Kisan Nafi’u: Kotu Ta Dage Shari’ar Hafsat Chuchu

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending