Connect with us

News

Yadda Mai Gadi Ya Harbe Sufeton ‘Yansanda Har Lahira A Jihar Adamawa

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

 

Advertisement

Wani mai gadi mai suna Andy Ukoh, ya harbe wani dan sanda mai suna Richard Felix, har lahira bisa kuskure yayin da yake kokarin kubutar da mamacin daga hannun mahara a Yola, a Jihar Adamawa.

Tun da farko wasu ‘yan ta’adda biyar sun kai wa marigayi Insfekta Felix hari, sai dai mai gadin ya harbe dan sandan bisa kuskure.

Advertisement

Ba Ministar Jin Ƙai Ce Kaɗai Ta Aikata Almundahanar Kuɗi Ba — Atiku Abubakar

Ukoh da daya daga cikin ‘yan ta’adda , Mordekai Elisha, an kama su, daga bisani kuma babbar kotun majistare ta I, ta tsare su bisa zargin hada baki, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma kisan kai.

Leadership ta ruwaito cewa Ukoh ya musanta aikata laifin, yayin da Mordekai ya amince da aikata laifukan.

Advertisement

An kashe marigayin ne a hanyarsa ta komawa gida a Jambutu, Karamar Hukumar Yola ta Arewa daura da wani otal a ranar 1 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 1:00 na dare.

Akalla mahara biyar ne suka bi sawun dan sandan, ciki har da Mordekai, jim kadan da barin harabar otal din.

Advertisement

Jami’in tsaron da ke gadin otal din, ya ga yadda ‘yan ta’addan suka kai wa dan sandan hari, inda ya yi kokarin ceto shi.

Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 18 ga watan Junairu, 2024.

Advertisement

A wani labarin kuma Ba Ministar Jin Ƙai Ce Kaɗai Ta Aikata Almundahanar Kuɗi Ba — Atiku Abubakar

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending