News
Ba mu da masaniya kan ficewar Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso – Ecowas
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ba ta samu sanarwa a hukumance ba game da ficewa mambobinta uku Nijar Mali da Burkina Faso ba.
Ƙasashen uku sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ne cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka karanta a gidan talabijin, inda suka zargi ƙungiyar da gazawa a taimaka musu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma matsalar tsaro.
Yadda Mutuwar Wani Matashi Ya Girgiza Jama’a Sakamakon Wasiyyar Da Ya Bar Wa Iyayen Sa
To sai dai cikin wata sanarwar da Ƙungiyar ta fitar da maraicen ranar Lahadi, ta ce babu wata katarda da ƙasashen suka aike mata bisa wannna aniya tasu. Ecowas ɗin ta ce tana aiki da waɗannan ƙasashen uku domin maido da su kan turbar dimokraɗiyya.
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙasashen uku na da matuƙar muhimmanci ga ƙungiyar, don haka take ƙoƙarin ganin ta lalubo hanyoyin warware matsalolin da ƙasashen ke fuskanta.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
