News
Yadda Mutuwar Wani Matashi Ya Girgiza Jama’a Sakamakon Wasiyyar Da Ya Bar Wa Iyayen Sa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wani Matashi mai suna Aminu Umar Faruq wanda ya yi fama da matsanancin ciwon ciki na kwana ɗaya Sakamakon wannan jinya ne Aminu ya aikewa iyayen sa da wasika yana mai neman gafarar su tare kuma da bayyana musu mutanen da ke binsa da kuma waɗanda shi yake bi bashi.
Ga abinda wasiƙar tace:
BABANA DA KUMA MAMANA, NA BARKU LAFIYA DOMIN WANI CIWON CIKI YA KAMANI, DA DADARE HAR NAFARA JIN ZAN IYA BARIN DUNIYAR NAN, TOOH GA WASIYA TA.
AUDU KWALI YANA BINA DUBU GOMA 10k, HARUNA MAI WANKIN HULA DUBU BIYU 2K.
NI KUMA INABIN ALH MAI KAYAN BOX NAIRA DUBU BIYAR 5k.
WANNA SHENI MABUDIN WAYA NA
Password – 491109 –
MUHIBBA NA BARKI LAFIYA INA KAUNAR KI SOSAI, WASSALAM.
Wikki Times ta ruwaito cewa Haƙika wannan wasika ta matukar girgiza mutane da dama inda suka yi ta alhini tare da yi masa fstan
