Opinion
Yadda Kasuwanci Ya Kasanci Bayan Dai Na Aikin Jigilar Jirgin Kasa Daga Nguru Zuwa Kano

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Yan kasuwa da matafiya na Jihar Kano da Kuma Nguru Sun fuskanci kalubale a akan Kasuwanci su na yau da kullum sakamakon dai na amfani da jirgin Kasa daga Nguru zuwa Kano yayi
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa halin dayan kasuwar suka shiga sakamakon tsayawar Jigilar jirgin kasan yankin nasu ya haifar da rashin aikin yi ga matasa da dama.
Haka zalika dubban mutane ne Suka rasa ayyukan yi yayin da farashin Kayaiyaki shima ya karu hakan ya tilastawa ya’n kasuwa dakon kayan su a mota
Majalisar Dattawa ta buƙaci zama da shugabannin tsaro kan tabarɓarewar tsaron ƙasa
Saidai al’umma da dama na ganin matsalar kamar tana barazana ga kasuwancin su duba da yanda matsalar tsaro ke damun kasar sakamakon indan da jirgin kasan mutum nasiyan kaya kuma a aikamasa da shi a cikin farashi mai sauki.
Muna mika sakon mu ga gwamnati data duba, halin da mutane suke ciki, ta dawo da Jigilar wannan jirgi, saboda mutanen da suke cin abinci a karkashin wannan jirgi da Kuma bunkasar tattalin arzikin Nigeria. Idan har tsadar farashin Gas ne, to me yasa sauran jirage suke aiki?
Wannan wata dama ce ga masu ruwa da tsaki a kan lamarin ,Don habbaka harkar kasuwanci a yankuna da lamarin yashafa, duk Wanda yayi hubbasa ya tsaya domin dawowar aikin wannan jirgi, tabbas zai samu karbuwa agurin yan kasuwa wannan yanki. Muna Adduar Ubangiji Allah yakawo karshen wannan matsala.