News
Wata mata ta yi yunƙurin sayar da ‘ya’yanta biyu kan N1.8m saboda tsadar rayuwa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Jihar Anambra ta cafke wata mata a jihar wadda ta yi yunkurin siyar da wasu ‘ya’yanta biyu maza daga cikin ‘ya’ya 11 da take da su.
Chinyere Chukwu wadda ‘yar asalin yankin Karamar Hukumar Ihiala ce a jihar, ta fada a komar hukuma ne ta hannun Ma’aikatar Harkokin Mata da Walwala ta Jihar.
Rahotanni na nuni da cewa matar ta hada baki ne da daya daga cikin ‘ya’yanta mata mai shekara 17 a kan su siyar da biyu daga cikin ‘ya’yan “saboda tsadar rayuwar da ake fama da ita a kasa.”
Chukwu ta shaida wa hukuma cewa, ta shirya sayar da ‘ya’yan nata ne bayan da ta ga cewa ta gaza daukar dawainiyarsu.
Ta ce, “Tun da yaran maza ne na yi nufin sayar da kowannensu ne kan farashi Naira miliyan 1, amma daga bisani muka tike a kan miliyan N1.8 su biyun maimakon miliyan N2.”
Kwamishinan Harkokin Mata ta Jihar, Ify Obinabo ce ta jagoranci jami’an tsaro zuwa damko matar da ake zargin a ranar Talata.
Daga bisani Obinabo ta bada umarnin akwashi ragowar ‘ya’yan zuwa karkashin kulawar gwamnatin jihar domin ba su kulawa yadda ya kamata.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
