News
Kotu ta umarci Gwamnatin Nijeriya ta daidaita farashin fetur, madara, sukari keke da sauransu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Legas ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako daya a kan ta daidaita kayayyakin masuru a fadin kasa don amfanin ‘yan kasa.
Kayayyakin da lamarin ya shafa sun hada da madara, sikari, gishiri, keken hauwa, babur, fetur, gas, kananzir da sauransu.
Kotun ta ba da wannan umarni a zaman da ta yi a ranar Laraba karkashin jagorancin Mai Shari’a Ambose Lewis-Allagoa.
Alkalin ya bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta daidaita farashin kayayyakin ne biyo bayan karar da Babban Lauyan Nijeriya kuam mai rajin kare hakkin dan’adam, Femi Falana SAN ya shigar Kotun.
A cewar Alkalin, “Na ji mai karar Femi Falana a cikin kararsa mai lamba FHC/L/CS/869/2023 kuma na gano duk da karar da aka shigar kan masu kare kansu, Atoni-Janar da Hukumar Kula da Farashi babu wata hammaya da aka samu dangane da haka, wanda haka doka ce cewa an amince da dukkan hujjojin da a ka gabatar.”
