Connect with us

News

Jami’an Rundunar Sojin Saman Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Yin Garkuwa Da Mutane A Kano 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Jami’an rundunar sojin saman Najeriya NAF sun kama wani matashi dan shekara 35 da ake zargi da yin garkuwa da mutane mai suna Isah Abdul, wanda ake kyautata zaton yana da hannu wajen yin garkuwa da mutane da dama a  garin Kano.

Advertisement

A cewar rundunar , an kama mutumin ne a ranar 19 ga watan Fabrairun 2024 da misalin karfe 6.30 na yamma a wani aiki na hadin gwiwa bayan samun bayanan sirri kan maboyar wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne da kungiyarsa.

Ƴan Najeriya sun mayar wa ɗan Tinubu martani bayan ya ce ‘a yi haƙuri da halin ƙunci’

Air Vice Marshal Edward Gabkwet, Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na Rundunar Sojojin Saman Najeriya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Advertisement

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a karamar hukumar  Takai a jihar Kano.

Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa Isah Abdul da ‘yan kungiyarsa ne ke da alhakin sace wani Yakubu Ibrahim Tagaho, wanda aka fi sani da “Sarkin Noman Gaya,” a ranar 6 ga Afrilu, 2023, daga ofishinsa.

Advertisement

 

 

Advertisement

Daily Post

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending