Connect with us

News

Tsadar Rayuwa: Al,umma sun jinginar da tukunyar Iskar gas ɗin su sun rungumi gawayi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wasu mazaunan Babban Birnin Tarayya, Abuja sun bayyana cewa tsananin tsadar rayuwa ya sa sun jinginar da tukwanen iskar gas ɗin su na girki sun rungumi girki da gawayi.

Dalilin yin haka kuwa na da nasaba ne da tsadar iskar gas da ake fama da shi yanzu.

NIN: Kimanin Mutane Miliyan 70 Ne Za Su Rasa Asusun Bankunan Su

Shi kansa farashin gawayin yayi sama daga naira 3,500 zuwa 4,000 ya koma naira 5,000 zuwa 6,000.

Wata mazauniyar gundumar Gwagwalada Victoria Amosu ta ce tun da gas ya kara kudi ta koma amfani da gawayi da itace.

Advertisement

Victoria ta ce a shekarar 2023 ta siya tukunyar gas mai nauyin 12.5 akan naira 12,000 zuwa 13,000 amma yanzu farashin sa ya kai naira 15,750 zuwa 16,000.

Wani dan kasuwa dake Unguwar Maraba mai suna Dayo Kunle ya ce iyalinsa na amfani da gawayi yanzu saboda yawansu ba zai iya jure siyar Gas ba a wannan lokaci da ake ciki.

“Mukan yi amfani da gas amma sai wajen dumamen abinci kokuma idan ya zama dole.

Premium Times ta ruwaito cewa Gloria Ikenna wace ke sana’ar abinci ta ce itama dole take amfani da gas duk da ko a kullum kaea kuɗi ya ke yi.

“Na bude gidan siyar da abinci a unguwar da aka hana girki da itace ko gawayi. Hakan ya sa dole na ke girki da Gas, kuma ribar da nake samu bai taka kara ya karya ba.

Gloria ta yi kira ga gwamnati da ta rage farashin gas domin tallafawa talakawa da masu sana’a irin nata.

Advertisement

Wata dake bautar kasa NYSC Ogechukwu Ukwuani ta ce tsadar farashin gas ya sa tana amfani da risho da kuma wuta.

“Matsalar ita ce idan aka dauke wuta dole na nemi wani abincin da zan ci domin ba zan iya girki ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending