Connect with us

News

Donald Trump na da cancantar ci gaba da takara – Kotun Ƙoli

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kotun ƙolin Amurka ta soke yunƙurin Colorado na haramta wa Donald Trump shiga zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa.

Babbar kotu a Colorado ta cire sunan tsohon shugaban ƙasar daga takardar ƙuri’a a Disamba inda ta kare matakinta da sashe na 14 na dokar haramcin da aka yi wa gyaran fuska kan masu tayar da rikici da ke neman tsayawa takara.

Kar Ku Rika Biyan Kudin Gyaran Transfoma —Kamfanin JED

Sai dai alƙalan kotun ƙolin na shakku game da matakin a wani zama da aka yi ranar 8 ga watan Fabarairu inda suka zargi jihar da wuce gona da iri.

Hakan na nufin Trump na iya shiga zaɓen fitar da gwani a gobe, a ranar da yake iya samun tikitin yi wa Republican takara.

Colorado za ta kaɗa ƙuri’a tare da wasu jihohi 15 a babbar ranar Talata mai muhimmanci a zaɓen 2024.

Advertisement

Ana sa ran Trump mai shekara 77 zai lashe zaɓen tare da kayar da abokiyar karawarsa ɗaya tilo, tsohuwar jakadar Majalisar Ɗinkin Duniya Nikki Haley.

 

Martanin Trump kan hukuncin kotu

 

Donald Trump ya mayar da martani game da hukuncin kotun ƙolin cewa Colorado ba za ta iya hana shi shiga zaɓen fitar da gwani ba.

“Babbar nasara ce ga Amurka!!!”, kamar yadda Trump ya wallafa a manhajarsa ta Truth Social

Advertisement

Bayan nan kuma tsohon shugaban ya aika wani saƙon Imel inda yake kira ga magoya bayansa su bayar da gudummawa a yaƙin neman zaɓensa.

“Ƙudurin Democrat na goge sunana bai yi nasara ba, amma yaƙinmu na ɗaukaka Amurka, ko kusa bai kare ba,” kamar yadda saƙon ya bayyana.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending