Business
A shirye bankunan Najeriya suke wajen cika sharuɗɗan ƙarfafa jarin su -ACAMB
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyar Ƙwararrun Jami’an Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Bankunan Najeriya, sun bayyana cewa lallai tabbas bankunan Najeriya za su iya cika sharuɗɗan ƙarfafa yawan jarin kuɗaɗen su, kamar yadda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarce su da yi.
A ranar 29 ga Maris ne CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci na Najeriya su ƙara yawan kuɗaɗen hada-hadar jarin su.
CBN ta umarci manyan bankuna masu lasisin yin hada-hada da kafa rassa a ƙasashen waje, su ƙara yawan jarin su zuwa Naira biliyan 500.
Su kuma bankunan cikin ƙasa kawai su ƙara yawan jarin su zuwa Naira biliyan 200. Bankunan shiyyoyi kuma an umarce su da su ƙara zuwa Naira biliyan 50.
Sanarwar da Shugaban Ƙungiyar ACAMB, Rasheed Bolarinwa ya fitar, ta ce ƙungiyar su ta yi marhabin da wannan sabon tsarin da CBN ya shigo da shi, wanda aka ce kowane banki ya cika waɗannan sharuɗɗa nan da watanni 24.
CBN ya umarci bankuna su ƙara yawan jarin hada-hadar bankunan su.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan Najeriya cewa kowane ya ƙara yawan jarin kuɗaɗen hada-hadar sa.
An buƙaci bankunan cewa kowane ya tabbatar da ya ƙara aƙalla adadin da aka umarce shi ya ƙara, nan zuwa watanni 24 masu zuwa.
Premium Times ta ruwaito cewa Cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta Riƙo ta CBN, Hakama Ali ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ana buƙatar ƙarfin jarin duk wani banki mai rassan hada-hada a ƙasashen waje ya kasance Naira biliyan 500, yayin da bankunan cikin ƙasa kawai ya kasance ƙarfin na da ƙarfin ƙarin Naira biliyan 200.
CBN ya ce ƙananan bankuna da ke yankunan ƙasar nan daban-daban kuma, na su ƙarfin jarin kada ya gaza Naira biliyan 50.
CBN ya ce an umarci kowane banki ya cika waɗannan sharuɗɗa nan da tsawon watanni 24 daga ranar 1 ga Afrilu. Wato kada wani banki ya wuce ranar 31 Ga Maris, 2026 bai cika sharuɗɗan ba.