News
Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun!!! Allah ya yiwa Dan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar Bagwai da Shanono Rasuwa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun!!!
Allah ya yiwa Dan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar Bagwai da Shanono, Hon Halilu Ibrahim Kundila rasuwa bayan gajeriyar jinya.
Ya rasu yana da shekara 62 a duniya ya bar mata 3 da Yara 22. Kafin rasuwarsa shi ne Dagacin garin Kundila dake Shanono.
Za’a yi jana’izarsa a gidansa dake garin Kundila na karamar hukumar Shanono a daidai wannan Lokaci, kamar yadda dattijon jam’iyyar APC na karamar Hukumar Bagwai, Bello Gogori ya tabbatar.
Allah ya gafarta masa zunubansa, in tamu tazo yasa mu cika da imani.
Advertisements
