Connect with us

News

Cutar Sanƙarau Ta Halaka Mutum 85 A Jihar  Yobe

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin jihar Yobe ta ce sanƙarau ta kashe mutum 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a jihar.

Advertisement

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Damaturu.

JAMB Ta Saki Sakamakon Jarrabawar UTME  Na  Shekarar 2024.

Ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke cewa cutar ta yi ajalin sama da yara 200 cikin mako biyu inda ya ce haƙiƙanin adadin shi ne 85.

Advertisement

Ya kuma ce fiye da marasa lafiya 2,510 da suka kamu da cutar a jihar sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.

Dakta Gana ya kuma ce an tura jami’an lafiya na sa kai sama da 200 zuwa sassan ƙananan hukumomin Poyiskum da Fika a wani ɓangare na ƙoƙarin da ma’aikatar take na daƙile cutar.

Advertisement

Ya ce ma’aikatan lafiya sun bi gida-gida domin ganowa tare da tura mutanen da ke da cutar asibiti.

Bbc Hausa ta ruwaito cewa yankunan arewacin Najeriya na fama da matsanancin zafi a tsukin nan – yanayin da ke haddasa cutar ta sanƙarau.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending